Mu Zagaya Duniya

Mu Zagaya Duniya

Shirin Mu Zagaya Duniya na duba Wasu Muhimman Labarai da suka ja hankalin Duniya a cikin mako. Ana gabatar da shirin ne a ranar Asabar da safe a kuma maimaita ranar Lahadi da daddare.

00:00
00:00

Короткий зміст епізоду

Shirin Mu Zagaya duniya na wannan mako tare da Oumarou Sani, ya yi duba kan sake rincaɓewar alaka tsakanin Nijar da Chadi bayan da Yamai ta zargi N'Djamena ta zargi da kashe yan kasarta biyu a wani harin da ta kai da jirgi mara matuki yankin Agadas Shiga alamar sauti don sauraron cikakken shirin....

Епізоди

567-

Dalilan da yasa dangantaka tsakanin Nijar da Chadi ta yi tsami

Shirin Mu Zagaya duniya na wannan mako tare da Oumarou Sani, ya yi duba kan sake rincaɓewar alaka tsakanin Nijar da Chadi bayan da Yamai ta zargi N'Djamena ta zargi da kashe yan kasarta biyu a wani harin da ta kai da jirgi mara matuki yankin Agadas Shiga alamar sauti don sauraron cikakken shirin....

31 жовт. 2026
566-

Gwamnatin Najeriya ta ce ta shirya tsaf don tunkarar barazanar Ebola

Shirin Mu zagaya Duniya na wannan makon tare da Oumarou Sani ya yi duba kan matakan da Najeriya ke ɗauka don hana yaduwar cutar Ebola a ƙasar. Shiga alamar sauti don sauraron cikakken shirin......

24 жовт. 2026
565-

Iran ta nesanta kanta daga rikicin da ke faruwa tsakanin yan Houthi da Saudia

Shirin Mu zagaya Duniya na wannan mako tare da Oumarou Sani ya duba lamurran siyasar Najeriya da kuma rincabe rikici tsakanin mayakan Houthi na Yamen da Saudia. Shiga alamar sauti don sauraron cikakken shirin......

17 жовт. 2026
564-

"Mu zagaya Duniya" bitar muhimman labaran da suka faru a makon da ya gabata

Kamar kowanne mako shirin "Mu zagaya Duniya" ya yi bitar muhimman labaran da suka faru a mako da muke bankwana da shi daga sassa daban-daban na duniya, ciki kuwa har da rikicin gabas ta tsakiya musamman yadda aka cika shekaru 3 cif da faro yaƙin Isra’ila a Gaza daya kashe fararen hula fiye da dubu 70 wanda kuma shi ya assasa sauran rikice-rikicen da ake gani a yankin, kana a Najeriya da Nijar muka duba halin da ake ciki game da tsadar man fetur sai kuma matsalar tsaro. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.....

10 жовт. 2026
563-

Shugaban Faransa ya bayyana halin da ake ciki a zirin Gaza a matsayin abin kunya ga duniya

A yau shirin ya yi waiwaye kan bankado yadda wasu fitattun yan siyasa a Najeriya suka wawure makudan kudade tare da mallakar kadarori a Amurka, sai Hukumar Lafiya ta Duniya WHO da ta fara gwajin allurar Ervebo don daƙile cutar Ebola a Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Congo, da kuma fassarar kalaman shugaban Faransa Emmanuel Macron a babban taron MDD da ya bayyana halin da ake ciki a zirin Gaza na Palasdinu a matsayin babban abin kunya ga ƙasashen duniya. Masu bincike da suka ɓanƙado yadda jami’an gwamnatin Najeriya na baya da na yanzu suka wawure makuɗan kuɗaɗen talakawa wajen sayen manyan gidaje na ƙasaita a Amurka, sun ce yaƙi da ta’addanci na daga cikin manyan hanyoyi da ake amfani da shi wajen satar dukiyar jama’a a Najeriya. Haka zalika, kotun sasanta rikicin kasuwancin ta duniya dake birnin Paris na Faransa, ta yi watsi da buƙatar Kamfanin Sunrise da ya nemi Najeriya ta biya shi diyyar kuɗi dala miliyan 400.

26 вер. 2026