Короткий зміст епізоду
Jamhuriyar Nijar, inda noman rani ranin ke fuskantar ƙalubale musamman a jihar Maraɗi, sakamakon karancin man fetur da kuma tsadarsa, lamarin da ya tilasta wa manoma dakatar da ayyukansu.
Jamhuriyar Nijar, inda noman rani ranin ke fuskantar ƙalubale musamman a jihar Maraɗi, sakamakon karancin man fetur da kuma tsadarsa, lamarin da ya tilasta wa manoma dakatar da ayyukansu.
Епізоди
Masu noman rani na fuskantar ƙalubale a jihar Maraɗi sakamakon karancin man fetur
ПрослуханоJamhuriyar Nijar, inda noman rani ranin ke fuskantar ƙalubale musamman a jihar Maraɗi, sakamakon karancin man fetur da kuma tsadarsa, lamarin da ya tilasta wa manoma dakatar da ayyukansu.
Najeriya ta karɓi baƙuncin taron Hukumomin Hasashen Yanayi na Duniya
ПрослуханоShirin Muhallinka Rayuwarka na wannan makon tare da Nura Ado Suleiman ya tattauna kan taron Hukumomin Hasashen Yanayi na Duniya, wanda a karon farko ya gudana a nahiyar Afrika, kuma Najeriya ta karɓi baƙuncinsa a birnin Legas. Shirin ya kuma tattauna kan yadda har yanzu manoma da dama a Najeriya ke da shakku kan nau'ikan irin shuka da aka inganta. Sai a ,atsa alamar sautin da ke sama domin sauraron shirin.......
Yadda matsalar tsuntsayen Jan Baki ta addabi manoma a jihar Jigawa
ПрослуханоShirin Muhallinka Rayuwarka na wannan mako ya yi duba ne kan matsalar tsuntsayen jan baki da ke lalata gona komai girmanta a duk lokacin da suka durfafeta a jihar Jigawa da ke Arewacin Najeriya, wadda ta yi ƙamarin da har wasu manoma na cewa, dabarun da suka daɗe suna amfani da su wajen korar tsuntsayen sun kasa magance matsalar, lamarin da ya tilasta musu neman wasu sabbin hanyoyi. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Nasiru Sani...........
Hukumar NIMET a Najeriya ta yi hasashen yiwuwar ambaliya a jihoh 13 na ƙasar
ПрослуханоA wannan makon shirin ya mayar da hankali ne kan duba sabon hasashen da Hukumar Hasashen Yanayi ta Najeriya ta yi, game da yiyuwar samun matsalar ambaliyar ruwa a wasu jihohi 13 na kasar a wannan damunar. A baya-bayan nan, hukumar hasashen yanayi ta Nigeria wato NIMET, ta sake fito da wani sabon hasashen yiyuwar ambaliyar ruwa a cikin watan Agustan wannan shekara, tsakanin ranar 11 zuwa 20 ga watan na Agusta, a wasu jihohi 13 na kasar. Cikin sanarwar da ta bayar, hukumar ta NIMET, ta bayyana cewa hasashen nata, ya dogara ne kan adadin ruwan saman da ake fatan samu, da yanayin kasa tare da girman magudanan ruwa da kuma yawaitar madatsun ruwa.
Matsalar ambaliyar ruwa da ake samu duk lokacin damina a ƙasashen Afrika
ПрослуханоShirin Muhallinka Rayuwarka na wannan mako ya yi duba ne kan matsalar ambaliyar ruwa da ake fuskanta kowace shekara lokacin damina a sassan ƙasashen Afrika. Kamar kowace shekara, a bana ma ana hasashen samun ambaliyar ruwa a wasu kasashen yammacin Afrika, inda akan samu rasa rayuka da dukiya mai tarin yawa. A Najeriya, an sha samun hasarar rayuka a sanadin matsalar ambaliyar ruwan, da kan rutsa da wasu yankunan kasar. Latsa alamar sauti don sauraren shirin...